Najeriya-Coronavirus

Tsoron kamuwa da COVID-19 ya janyo yawaitar mace-mace a Najeriya - Gwamnati

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari RFI Hausa

Gwamnatin Najeriya ta bayyana damuwa kan yawaitar mace-macen da ake samu a wasu jihohin kasar musamman na yankin arewaci, wadanda tace suna da nasaba da annobar coronavirus, sai dai ba kai tsaye ba.

Talla

Yayin karin bayanin da ya saba yi a kowace rana kan halin da ake ciki dangane da yakar cutar coronavirus a Abuja, Ministan Lafiyar Najeriya dakta Osagie Ehanire, yace mafi akasarin mace-macen da aka samu a baya bayan nan cikin wasu jihohi, sun auku ne saboda tsoron zuwa asibiti da shiga zuciyoyin jama’a da dama, inda ya kamata su samu kulawa kan matsalar dake damunsu, to amma tun bayan bullar annobar COVID-19 da dama suka kauracewa asibitoci bisa fargabar kada gwaji ya nuna sun kamu da cutar.

A gefe guda Ministan Lafiyar ya kuma bayyana bakuwar halayyar kin karbar marasa lafiya ko basu kulawa, da wasu jami’an lafiya ciki harda likitoci suka dauka saboda tsoron kamuwa da cutar coronavirus, a matsayin karin dalilin da ya janyo mutuwar mutane da dama cikin kankanin lokaci a sassan Najeriya, ciki harda Jigawa, Kano, Yobe da kuma Azare dake Bauchi.

Dakta Osagie Ehanire yace sakamakon binciken da suka gudanar a baya baya nan ya nuna cewar, adadin mata masu ciki dake zuwa awo ya ragu da sama da kashi 50 cikin 100, kwatankwacin raguwa daga adadin mata miliyan 1 da dubu 300, zuwa mata masu juna biyu dubu 655, yayinda kuma adadin matan dake zuwa asibiti domin haihuwa ya ragu daga miliyan 4 zuwa miliyan 2 a fadin Najeriya.

Binciken da hukumar Najeriya mai tattara bayanan alkalumman da suka shafi fannin lafiya ta gudanar, ya kuma gano cewar, adadin kananan yaran da ake kaiwa asibiti domin samun allurorin rigakafi shi ma da ya ragu da kusan kashi 50, yayinda yawan mutanen dake zuwa asibiti don duba lafiyarsu bisa ra’ayinsu ya ragu daga akalla dubu 158 da 374, zuwa kasa da dubu 99.

Yanzu haka dai kwararru na bincike kan yawatar mace-macen da aka samu cikin kankanin lokaci a sassan Najeriyar, inda wasu ke fargabar akwai alaka tsakanin annobar COVID-19 da mutuwar mutanen da dama, yayinda a nata bangaren gwamnati ta musanta zargin, tare da bayyana tsananin zafi, da wasu cutukan a matsayin musababbin yawaitar mace-macen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.