Buhari ba zai yiwa 'yan Najeriya jawabi kan coronavirus a yau ba - Adeshina
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Fadar gwamnatin Najeriya tace shugaban kasar Muhammadu Buhari ba zai yiwa ‘yan kasar jawabi kan annobar coronavirus a yau ba, kamar yadda aka zata da fari, inda a yau ake dakon sanin makomar matakan cigaba da sassauta dokar hana fita ko akasin haka.
Mai baiwa shugaba Buhari shawara na musamman kan kafafen yada labarai Femi Adeshina ne ya bayyana haka a yau litinin cikin sanarwar da ya wallafa ta shafinsa na twitter.
Adeshina yace a maimakon Buhari, shugaban kwamitin yaki da annobar coronavirus kuma sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya Boss Mustapha ne zai yi karin haske kan halin da ake ciki, da kuma matakan da gwamnati ta yanke shawarar dauka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu