Najeriya-Coronavirus

Buhari zai yi jawabi kan makomar sassauta dokar hana fita

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Nigeria Presidency/Handout via REUTERS

Yau litinin ake sa ran shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabi ga ‘yan kasar kan makomar matakin sassauta dokar hana-zirga-zirgar da gwamnati ta dauka a sassa daban daban, matakin da a baya ta dauka domin dakile yaduwar annobar coronavirus.

Talla

Daya daga cikin manyan jami’an lura da gudanarwar ayyukan kwamitin da gwamnatin Najeriya ta kafa don yakar annobar coronavirus a kasar, Aliyu Sani ne ya sanar da shirin jawabin na shugaba Buhari a yau, yayin tattaunawa da da kafar talabijin na Channels a ranar lahadin karshen makon nan.

Sani yace kwararru na bibiyar yadda lamurra ke gudana tun bayanda gwamnati ta sassauta dokar hana fita a jihohin Legas, Ogun da kuma birnin Abuja, da ma a wasu karin jihohin da gwamnatocinsu suka sassauta bada damar fita a wasu kwanaki, inda yace akwai damuwa kan yadda ‘yan Najeriya da dama suka rika bijirewa sharuddan, sanya takunkumi, da tsarin nesa-nesa da juna, da likitoci suka gindaya na kiyaye yaduwar annobar coronavirus.

Makwanni biyu da suka gabata ne dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bada umarnin killace jihar Kano baki daya, ba shiga ba fita, da kuma hana zirga-zirga a cikin jihar, domin dakile yaduwa annobar coronavirus da ta bulla cikinta, inda zuwa yanzu sama da mutane 700 suka kamu da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.