Najeriya-Kano

Ganduje ya baiwa al'ummar Kano damar yin Sallar Idi

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Solacebase

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da matakin baiwa al'ummar jihar damar yin sallar Idi.

Talla

Ganduje ya sanar da daukar matakin ne bayan cimma matsaya da Malamai da sauran masu ruwa da tsaki yayin ganawar da suka yi a yau litinin, bisa sharadin daukar matakan kare yaduwar annobar coronavirus yayin gudanar da ibadar ta Sallah Karama. Sai dai ba za a yi bikin hawan Sallah kamar yadda aka saba ba.

Gwamnan ya kuma sanar da janye dokar hana yin Sallar Juma'a da ta shafe makwanni tana aiki domin dakile yaduwar cutar ta coronavirus.

A karkashin sharuddan da gwamnati ta gindaya, Sallar Juma’ar za ta rika gudana ne a karkasin kulawar jami’an hukumar Hizbah, wadanda za su tabbatar da cewar mutane sun kiyaye dokokin tsafta da sauran sharuddan da kwararru suka gindaya.

Ganduje ya kuma yi karin bayanin cewar daga yanzu za a sassauta dokar hana zirga-zirga a jihar ta Kano, inda za a baiwa jama’a damar fita sau uku a mako, a ranakun Litinin, Laraba da kuam Juma’a daga karfe 10 na safiya zuwa 6 na yammaci.

AbdoulKareem Ibrahim Shikal ya tattauna da Hon Muktar Ishaq Yakasai, kwamishinan ayyuka na musamman a jihar ta Kano.

Hon Muktar Ishaq Kwamishinan ayyuka na musamman kan baiwa al'ummar Kano damar yin Sallar Idi

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.