Najeriya-Coronavirus

Gwamnati ta kara wa'adin dokar killace Kano da tsawon makwanni 2

Boss Mustapha, Sakataren Gwamnatin Najeriya, kuma shugaban kwamitin yaki da annobar coronavirus a kasar. (Daga bangaren dama)
Boss Mustapha, Sakataren Gwamnatin Najeriya, kuma shugaban kwamitin yaki da annobar coronavirus a kasar. (Daga bangaren dama) © Nigeria Presidency

Kwamitin da gwamnatin Najeriya ta kafa don yakar annobar coronavirus a kasar, ya sanar da kara wa’adin dokar kulle daukacin jihar Kano daga shiga ko fita, da kuma hana zirga-zirga a cikinta da tsawon makwanni 2, idan aka dauke zababbun ranakun da aka sassautawa jama’a fita harkokin yau da kullum.

Talla

Sanarwar tace sabuwar dokar za ta soma aiki ne daga karfe 12 na daren yau litinin 18 ga watan Mayu.

Shugaban kwamitin yaki da annobar ta coronavirus, kuma sakataren gwamnatin Najeriya Boss Mustapha ne ya bayyana daukar matakin yau litinin a Abuja, yayinda yake karin bayanin da ya saba yiwa al’ummar Najeriyar kan halin da ake ciki, dangane da yaki da cutar.

Ranar 27 ga watan Afrilun da ya gabata, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bada umarnin killace jihar Kano na tsawon makwanni 2, matakin da yace zai taimakawa tawagar kwararrun lkitocin da aka aike dasu zuwa jihar, wajen kawo karshen yaduwar annobar coronavirus da ta bulla a cikinta.

Cikin rahotonta na baya bayan nan, hukumar yaki da yaduwar cutuka ta Najeriya tace jumilar yawan wadanda suka kamu da cutar coronavirus a Kano ya kai 825, daga cikinsu kuma 111 sun warke, yayinda 36 suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.