Najeriya-Coronavirus

Najeriya ta kama jirgin saman Birtaniya bisa karya dokar hana jigilar fasinja

Jirgin saman kamfanin Flair Aviation dake Birtaniya da Najeriya ta kama bisa karya dokar haramta jigilar fasinjoji zuwa ciki da wajen kasar.
Jirgin saman kamfanin Flair Aviation dake Birtaniya da Najeriya ta kama bisa karya dokar haramta jigilar fasinjoji zuwa ciki da wajen kasar. Solacebase

Gwamnatin Najeriya ta sanar da kama wani jirgin sama mallakin wani kamfanin kasar Birtaniya, bisa samunsa da laifin fasa kaurin jigilar fasinoji zuwa ciki da wajen Najeriya, duk kuwa da cewar gwamnati bata janye dokar haramta zirga-zirgar jiragen saman fasinja ba da ta kafa a makwannin baya, don dakile yaduwar annobar coronavirus.

Talla

A sanarwar da ya wallafa ta shafinsa na twitter ministan sufurin jiragen saman Najeriya Hadi Sirika, yace tun farko kamfanin mai suna ‘Flair Aviation’ ya samu amincewar gwamnatin Najeriya ne domin jigilar magunguna da sauran kayayyakin agaji zuwa cikin kasar, amma aka bankado cewar yana amfani da damar wajen cusa fasinjoji a boye, yana kuma shigar dasu Najeriya.

Sirika ya sha alwashin tabbagar da ganin kamfanin jiragen saman na Flair Aviation ya fuskanci hukuncin da ya dace bisa gagarumin laifin da ya aikata.

A karshen watan Maris gwamnatin Najeriya ta sanar da rufe dukkanin filayen jiragen samanta na kasa da kasa, domin dakile yaduwar cutar coronavirus, bayan karewar wa’adin dokar haramta zirga-zirgar jiragen ce, gwamnati ta kara wa’adinta da tsawon karin makwanni 4 cikin wannan wata na Mayu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.