Najeriya-Coronavirus

Adadin masu cutar coronavirus a Najeriya ya zarta dubu 6

Wani jami'in kiwon lafiya a birnin Abuja dake Najeriya, yayin yiwa wata mata gwajin cutar coronavirus.
Wani jami'in kiwon lafiya a birnin Abuja dake Najeriya, yayin yiwa wata mata gwajin cutar coronavirus. AFP

Hukumar yaki da yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC tace karin mutane 216 sun kamu da cutar coronavirus a kasar.

Talla

Rahoton da hukumar ta NCDC ta wallafa a daren jiya litinin, ya nuna cewar an samu sabbin kamuwar ne a jihohin Najeriya 15.

Legas ke da adadi mafi yawa na karin masu cutar ta corona da aka samu da adadin mutane 74, sai Katsina mai 33, Oyo 19, Kano 17, Edo 13, Zamfara mutane 10, yayinda Ogun, Borno da Gombe dukkaninsu ke da mutane 8-8.

Sauran jihohin sun hada da Bauchi da Kwara masu mutane 7-7, Abuja 4, Kaduna da Enugu 3-3, sai jihar Rivers da ta samu karin mutane 2.

Zuwa yanzu jumillar yawan mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya kai dubu 6 da 175, daga cikinsu kuma dubu 1 da 644 sun warke, yayinda 191 suka mutu.

Har aynzu Legas ke sahun gaba wajen yawan wadanda cutar ta COVID-19 ta kama da adadin dubu 2 da 550, daga cikinsu kuma 556 sun warke, yayinda 36 suka mutu, sai kuma Kano mai yawan mutane 825, daga ciki 111 sun warke, yayinda 36 suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.