Duniya

COVID-19 ta ki yiwa al'ummar duniya rangwame

Likitoci yayin kula da masu coronavirus a wani asibiti dake lardin Hubei a kasar China.
Likitoci yayin kula da masu coronavirus a wani asibiti dake lardin Hubei a kasar China. AP

Hukumomin Lafiya sun ce adadin mutanen da annobar COVID-19 ta kashe a fadin duniya sun zarta dubu 316, yawan wadanda suka kamu da cutar a yanzu kuma ya haura miliyan 4 da dubu 750.

Talla

Alkalumman baya bayan nan da hukumomin lafiyar na kasa da kasa suka fitar, sun nuna cewar tun bayan bullarta daga China a watan Disambar bara, coronavirus ta halaka jumillar mutane dubu 316 da 333, daga cikin miliyan 4 da dubu 759 da 650 da ta kama a fadin duniya, yayinda akalla mutane miliyan 1 da dubu 711 da 900 sun warke daga cutar.

Cikin awanni 24 da suka gabata, kididdigar jami’a lafiya ta nuna cewa mutane dubu 2 da 719 annobar ta halaka a fadin duniya, yayinda karin mutane dubu 77 da 737 suka kamu da cutar.

A Amurka annobar ta halaka mutane dubu 89 da 874, a Birtaniya mutane dubu 34,796 cutar ta kashe, sai Italiya mai mutane 32,007, Faransa ta rasa mutane dubu 28 da 239, yayinda a Spain cutar ta kashe mutane dubu 27 da 709.

A dunkule Nahiyar Kudancin Amurka ta rasa mutane dubu 29 da 522, Asiya mutane dubu 12 da 449, Gabas ta Tsakiya kuma dubu 8 da 234, yayinda Afrika ta rasa mutane dubu 2 da 793.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.