Bakonmu a Yau

Dakta Bashir Kurfi kan tasirin tsawaita wa'adin matakan yakar coronavirus kan tattalin arzikin Najeriya

Sauti 03:37
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Solacebase

Gwamnatin Najeriya ta sanar da Karin wa’adin hana zirga-zirga a tsakanin jihohin kasar da tsawon makwanni, gami da jinkirta daukan sauran matakan cigaba da sassauta takaita gudanar harkokin yau da kullum domin dakile yaduwar annobar coronavirus.Dangane da wannan mataki Garba Aliyu Zaria ya tattauna da Dakta Bashir Kurfi masanin tattalin arziki a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, kan tasirin matakin bisa tattalin arziki Najeriya.