Najeriya-Coronavirus

Jihohin Legas, Kano da Borno ke da kashi 52 na mutanen da corona ta halaka a Najeriya

Misalin fasalin kwayar cutar Coronavirus da aka yi amfani da Komfuta wajen fitarwa.
Misalin fasalin kwayar cutar Coronavirus da aka yi amfani da Komfuta wajen fitarwa. NEXU Science Communication/via REUTERS

Karamin ministan lafiya na Najeriya dakta Olorunnimbe Mamora, yace kashi 52 cikin 100 na yawan wadanda annobar coronavirus ke halakawa a fadin kasar sun fito ne daga jihohin Legas Borno da kuma Kano.

Talla

Dakta Mamora ya sanar da sakamakon kididdigar ce a jiya litinin, yayin taron manema labarai da kwamitin yakar annobar coronavirus ta gwamnatin Najeriya ta kafa ya saba yi duk rana a Abuja.

A bangaren adadin wadanda cutar ta coronavirus ta kama a fadin kasar kuma, shugaban kwamitin yakar annobar, zalika sakataren gwamnatin Najeriya Boss Mustapha, yace kananan hukumomi 9 daga cikin sama da 700 a fadin kasar, ke da kaso 51 na jumillar yawan wadanda cutar coronavirus din ta kama.

Dangane da karfafa ayyukan yiwa mutane gwajin cutar kuma, Boss Pustapha yace gwamnati ta samu nasarar kara yawan dakunan gwaje-gwaje daga guda 15 a fadin Najeriya zuwa 26, abinda ya bada damar yiwa jumillar mutane dubu 35 da 98 gwaji a yanzu haka.

A litinin din da ta gabata, 18 ga watan Mayu, gwamnatin Najeriya ta hannun kwamitin nata na yakar annobar coronavirus, ya sanar da kara wa’adin hana zirga-zirga tsakanin jihohi da makwanni 2, sai kuma Kano da aka tsawaita wa’adin killace ta da mako biyun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.