Najeriya-Kaduna

Babu ranar janye dokar hana fita a Kaduna - El-Rufa'i

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai.
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai. REUTERS/Afolabi Sotunde

Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i, yace babu ranar janye dokar hana fitar da ya kafa a daukacin jihar don dakile yaduwar annobar coronavirus.

Talla

El-Rufa’i yayi gargadin ne a lokacin da yake ganawa da wasu kafafen yada labarai dake jihar ta Kaduna a jiya Talata, inda yace ba shakkah akwai shiri a kasa na sassautawa da ma janye dokar hana jama’a fita baki daya, amma gwamnati ba ta soma nazari kan ranar aiwatar da matakin ba.

Gwamna Nasir El-Rufa'i yace kafin tunanin tsayar da ranar sassautawa ko janye dokar hana fita a Kaduna, tilas sai wadansu ka’idoji sun cika, da suka hada da kara yawan mutanen da jami’an lafiya ke yiwa gwajin cutar coronavirus a jihar, da kuma tabbatar da cewa an tabbatar da aikin dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohin Najeriya.

Bayaga kin amsa kiraye-kirayen bangarori da dama na al’umma kan baiwa jama’a damar yin Sallar Idi a ranar asabar ko lahadi dake tafe, El-Rufa’i ya sha alwashin cewar da kansa zai yi tattaki zuwa kan iyakar Kaduna da Kano don gudanar da sintirin tabbatar da cewar, babu wanda ya ketara zuwa cikin jiharsa daga birnin na Kano, a matsayin karin matakin yakar annobar coronavirus.

A halin da ake ciki, Kaduna ta shafe kusan wata 1 a killace, la’akari da cewar tun a ranar 26 ga watan Maris, El-Rufa’i ya kafa dokar hana fita a jihar, daga bisani kuma ya tsawaita dokar da karin wata 1 a ranar 26 ga watan Afrilu, domin dakile yaduwar cutar coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.