Najeriya-Coronavirus

Gwamnatin Najeriya ta bukaci 'yan kasar su fifita lafiyarsu sama da tattalin arziki

Boss Mustapha, Sakataren Gwamnatin Najeriya, kuma shugaban kwamitin yaki da annobar coronavirus a kasar.
Boss Mustapha, Sakataren Gwamnatin Najeriya, kuma shugaban kwamitin yaki da annobar coronavirus a kasar. PM News

Gwamnatin Najeriya ta bukaci al'ummar kasar da su fifita kare lafiya da rayukansu, sama da hankoron ganin gwamnati ta janye dokar takaita zirga-zirgar da ta kafa don dakile annobar coronavirus.

Talla

Sakataren gwamnatin Najeriya kuma shugaban kwamitin yaki da coronavirus Boss Mustapha ne ya bayyana haka, inda yace, gwamnati na da shirin sake bude harkokin tattalin arziki kamar da, amma sai jama’a sun kiyaye sharuddan da kwararru suka gindaya don kare yaduwar annobar.

Wannan na zuwa ne bayanda gwamnatin ta yanke shawarar daukar matakin cigaba da takaita harkokin yau da kullum da hana zirga-zirga tsakanin jihohi, da karin makwanni 2.

A halin da ake ciki, cibiyar yaki da yaduwar cutuka ta Najeriyar NCDC, tace adadin wadanda suka harbu da cutar coronavirus a fadin kasar ya haura zuwa dubu 6 da 401, bayan samun karin mutane 226 da suka kamu da cutar a jiya Talata, yayinda adadin wadanda suka mutu ya kai mutane 192.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.