Nijar-Najeriya

Nijar ta caccaki Najeriya kan gaza magance matsalar 'yan bindiga

Daya daga cikin dubban Iyalai 'yan Najeriya da hare-haren 'yan bindiga ya tilastawa tserewa daga muhallansu zuwa Jamhuriyar Nijar.
Daya daga cikin dubban Iyalai 'yan Najeriya da hare-haren 'yan bindiga ya tilastawa tserewa daga muhallansu zuwa Jamhuriyar Nijar. © UNHCR/Hélène Caux

Fuskantar karuwar hare-haren ‘yan bindiga a sassan Nijar dake iyaka da Najeriya a baya bayan nan, ya sanya wasu shugabannin al’umma zargin takwarorinsu dake bangaren Najeriya da hannu wajen ayyukan ta’adancin da yankin Maradi ke fuskanta.

Talla

Yayin zantawa da sashin Hausa na RFI, gwamnan Maradi Zakari Umaru, yace kawo yanzu ba za su iya tantance adadin dubban dabbobin da ‘yan bindiga suka sace daga yankunan dake jihar ta Maradi, sai dai za a iya kiyasta cewar yawan dabbobin ya kai dubu 50.

Wannan ce ta sanya gwamnan na Maradi zargin cewar akwai hannun wasu mahukunta ko sarakunan gargajiya da suke da masaniya kan karuwar hare-haren ‘yan bindigar daga bangaren Najeriya, wadanda kuma ke amfana da dubban dabbobin da ake sacewa daga kasar Nijar zuwa cikin Najeriya.

Rahotanni sun ce a yayinda hukumomin Jamhuriyar ta Nijar ke fafutukar magance matsalar hare-haren ‘yan bindigar dake ketarawa cikin kasar daga Najeriya, daruruwan ‘yan gudun hijira daga kasar ta Najeriya na cigaba da kwarara zuwa yankunan Nijar dake kan iyaka.

A makon da ya gabata, 12 ga watan Mayu, hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla fararen hula dubu 42 ne suka tserewa hare-haren ‘yan bindiga daga kauyukan kan iyakar kasashen Najeriya da Nijar.

Cikin bayanan da hukumar ta wallafa a shafinta, ta ce adadin kari ne kan wasu mutanen dubu 23 da karancin tsaro ya tilastawa tserewa daga yankunansu akan iyakar Najeriya cikin watan jiya, yayinda wasu karin fararen hula dubu 19 a Jamhuriyyar Nijar suka rasa matsugunansu wanda ke da nasaba da karancin tsaron da garuruwan kan iyaka ke fuskanta a kasashen biyu.

A sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce sakamakon tsoro da gujewa matsalar rashin tsaro a kan iyakokin kasar Nijar, ya tilastawa wasu al'ummar kasar dubu 19 zama yan gudun hijira a cikin kasarsu ta asali.

Wasu majiyoyi daga kan iyakar ta Najeriya da Nijar sun ce a halin da ake ciki, wasu daga cikin mazauna yankunan karkara na tara makamai na gargajiya ciki har da bindigogi kirar gida domin kare kai, abinda ake fargabar ka iya haifar da matsalar jama’a su rika daukar doka a hannu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.