Najeriya-Bauchi

COVID-19: Gwamnan Bauchi ya sassauta dokar hana zirga-zirga da tarukan addini

Gwamnan JIhar Bauchi Sanata Bala Muhammad.
Gwamnan JIhar Bauchi Sanata Bala Muhammad. RFI Hausa / Shehu Saulawa

Gwamnan Bauchi Sanata Bala Muhammed ya sassauta dokar hana zirga-zirga da tarukan jama’a a daukacin jihar, matakin da a baya aka dauka don dakile yaduwar annobar coronavirus.

Talla

Gwamnan ya dauki matakin ne bayan ganawa da malaman addini, sarakunan gargajiya, da sauran masu ruwa da tsaki.

Sanata Bala Muhammed, yace gwamnati da taimakon kwararru jami’an lafiya sun samu nasarar dakusar da kaifin annobar ta coronavirus, wadda a halin yanzu jumillar mutane 225 suka kamu da cutar, 127 daga cikinsu kuma suka warke, yayinda mutane 5 suka mutu.

Sassauta dokar hana zirga-zirgar da tarukan addinin ta soma aiki ne daga yau Alhamis, sai dai gwamnan Bauchin, yace dokar hana fita ko shiga cikin jihar na nan daram, makarantu za su cigaba da kasancewa a rufe, sai kuma takaita yawan fasinjojin da ake dauka a motocin haya da babur mai kafa uku, yayinda dokar haramta baburan haya na Okada take a matsayin ta dindindin.

Zalika dokar hana zirga-zirga daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe za ta cigaba da aiki, kamar yadda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bada umarni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.