Kano-Coronavirus

Likitoci da sauran jami'an lafiya 40 sun warke daga cutar coronavirus a Kano

Cibiyar killace masu cutar coronavirus dake Kwanar Dawaki, a Jihar Kano.
Cibiyar killace masu cutar coronavirus dake Kwanar Dawaki, a Jihar Kano. RFI Hausa / Abubakar Dangambo

Gwamnatin Kano ta sanar da sallamar likitoci da wasu ma'aikatan lafiya 40 daga cikin 50 da suka kamu da cutar coronavirus a jihar, bayanda gwaji ya tabbatar da cewar sun warke daga cutar.

Talla

Kimanin makwanni 3 da suka gabata likitocin da jami'an lafiyar dake aiki a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano suka harbu da cutar.

Yanzu haka kuma ma'aikatan lafiyar 10 ne suka rage a cibiyar killace masu dauke da cutar coronavirus, wadanda kuma hukumomin lafiya a Kano suka bayyana fatan sallamarsu nan da wani gajeren lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.