Najeriya-Lagos

Likitoci sun janye yajin aikin da suka soma a Legas

Wasu likitoci a Najeriya. (An yi amfani da wannan hoto domin misali)
Wasu likitoci a Najeriya. (An yi amfani da wannan hoto domin misali) Lagos Television

Kungiyar likitocin Najeriya ta janye yajin aikin da ta shiga a Legas, bayan sa’o’i 24 da daukar matakin.

Talla

A jiya Laraba kungiyar likitocin reshen Legas ta baiwa ‘ya’yanta umarnin soma yajin aikin sai baba-ta-gani, domin nuna rashin amincewarsu da cin zarafinsu da wasu jami’an tsaro ke yi, idan dokar hana fitar dare ta soma aiki a jihar daga karfe 8 zuwa 6 na safe, duk cewar basa daga cikin ma’aikatan da dokar ta shafa.

Daya daga cikin misalan da likitocin suka bayar dai shi ne yadda a wani lokaci jami’an tsaron suka hana wata motar daukar mara lafiya wucewa, gami da tsare ma’aikatan jinyar dake ciki zuwa wasu sa’o’i saboda zirga-zirga cikin dare.

Kafin janye yajin aikin, sai da gwamnatin Legas gami da rundunar ‘yan sandan jihar ta nemi afuwar likitocin kan yi musu ba daidai ba, inda suka sha alwashin hakan ba za ta sake faruwa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.