Najeriya-Lagos

Likitoci sun shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a Legas

Harabar wani asibiti dake birnin Legas.
Harabar wani asibiti dake birnin Legas. Afolabi Sotunde/Reuters

Kungiyar likitocin Najeriya reshen Legas ta shiga yajin aikin sai baba-ta-gani, bayanda a jiya Laraba ta baiwa ‘ya’yanta umarnin daukar matakin ta hanyar zama a gida.

Talla

Yajin aikin dai ya soma ne daga karfe 6 na yammacin ranar ta Laraba.

Sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar likitocin ta kasa reshen Legas, dakta Moronkola Ramon, tace shiga yajin aikin ya zama dole la’akari da yadda jami’an tsaro suke cin zarafin likitocin dake kokarin isa wuraren aiki ko komawa gidajensu, a daidai lokacin da dokar hana zirga-zirga ta soma aiki daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe a jihar ta Legas.

Tun farko dai yayin sanar da kafa dokar hana zirga-zirga don yakar annobar coronavirus, da kuma lokacin sanar da sassauta dokar, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya zayyana daidaikun mutane ko ma’aikatan da dokar hana fitar bata shafa ba, cikinsu harda likitoci.

Bayaga likitoci da sauran jami’an lafiya, bangarorin da dokar hana fitar bata shafa ba sun hada da ‘yan jarida, ma’aikatan gona, fannin man fetur da sauran masu ayyukan da al’umma ke cikin bukatarsu.

Hamza Alhassan, mazaunin Jihar Legas yayi tsokaci a kan yadda labarin ya riske su

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.