Sarkin Gwando na 19 Alhaji Mustafa Haruna Jakolo kan koma-bayan sha'anin tsaro a Najeriya

Sauti 04:11
Wasu yankunan arewa maso yammacin Najeriya na fama da hare-haren 'yan bindiga.
Wasu yankunan arewa maso yammacin Najeriya na fama da hare-haren 'yan bindiga. Information Nigeria

Matsalolin rashin tsaro a yankunan jihohin arewa maso yammacin Najeriya na cigaba da ciwa ‘yan asalin yankin tuwo a kwarya, kasancewar a duk rana sai kara samun munanan hare-hare ake daga ‘yan bindiga duk da matakan tsaron da ake dauka.Kan sha’anin tsaron ne Garba Aliyu Zaria ya tattauna da mai martaba Sarkin Gwandu na 19, kuma tsohon mai tsaron lafiyar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a zamanin mulkin soja, Alhaji Mustapha Haruna Jokolo, wanda yayi tsokaci kan halin da ake ciki da kuma mafita daga matsalar tsaron.