Najeriya

Coronavirus: Buhari zai Sallar Idi tare da iyalinsa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da iyalinsa.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da iyalinsa. Photo credit: Twitter / @MBuhari

Fadar gwamnatin Najeriya ta ce shugaban kasar Muhammadu Buhari zai yi Sallar Idin bana a gida tare da Iyalinsa a matsayin matakin kare yaduwar cutar coronavirus, kamar yadda kwararru a fannin lafiya suka bukata.

Talla

Bisa ga koyarwar Addini da kuma al’ada dai, dubban mutane ke halartar Sallar Idi a Masallatan da aka bada damar gudanar Ibadar a cikinsu, bayan kawo karshen Ibadar Azumin watan Ramadana.

A tsakanin ranakun Asabar ko Lahadin nan ake sa ran al’ummar Musulmi su gudanar da Sallar Idi karama a fadin duniya.

Sallar ta bana dai na zuwa ne a daidai lokacinda da duniya ke fuskantar annobar coronavirus da zuwa wannan lokaci ta halaka mutane akalla dubu 332 a tsakaniin kasashe kusan 200, ciki harda Najeriya.

Cikin sanarwar da fadar gwamnatin Najeriya ta fitar, ta ce matakin shugaba Muhammadu Buhari na yin Sallar Idi a gida biyayya ne ga umarnin mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III, wanda ya baiwa daukacin al’ummar Musulmin Najeriya umarnin yin Sallar a gida tare da iyalansu, don kare yaduwar cutar coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI