Najeriya

Sarkin Musulmin Najeriya ya bada umarnin yin Sallar Idi a gida

Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Sultan Sa'ad Abubakar III
Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Sultan Sa'ad Abubakar III YouTube

Majalisar Koli ta malaman addinin Musulunci a Najeriya dake karkashin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Sa'ad Abubakar III, ta bukaci al'ummar Musulmin kasar da su gudanar da Sallar Idi a gida, domin samun kariya daga annobar coronavirus.

Talla

Mai Alfarma Sarkin Musulmin ne ya sanar da umarnin, bayan kammala zaman tattaunawa kan halin da ake ciki, da majalisar koli ta malaman addinin Musulunci a kasar.

Yayin zantawa da sashin Hausa na RFI, babban sakataren kungiyar Jama’atul Nasril Islam Dakta Khalid Abubakar Aliyu, yace kwamitin bayar da fatawa kan sha’anin addini da ya kunshi fitattun malamai Malamai ne ya cimma matsayar ta cewa Musulmi su yi hakuri su gudanar da Sallar Idi a gida, la’akari da cewar akwai gamsassun hujjojin da suka bada damar yin hakan.

Babban Sakataren Kungiyar Jama’atul Nasril Islam Dakta Khalid Abubakar Aliyu kan umarnin Sarkin Musulmin Najeriya na yin Sallar Idi a gida

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.