Najeriya-Coronavirus

Yawan masu cutar coronavirus a Najeriya ya zarta dubu 7

Wasu 'yan kungiyar agaji yayin rabawa marasa karfi tallafi a birnin Legas.
Wasu 'yan kungiyar agaji yayin rabawa marasa karfi tallafi a birnin Legas. REUTERS / Temilade Adelaja

Cibiyar yaki da yaduwar cutuka a Najeriya NCDC, tace jumillar yawan wadanda suka kamu da cutar coronavirus a kasar ya kai dubu 7 da 16, bayan samun karin mutane 339 da suka kamu da cutar cikin sa’o’i 24 da suka gabata, tare da hasarar rayuka 9.

Talla

Cibiyar ta NCDC tace an samu sabbin mutanen da suka kamu da cutar ta coronavirus ce a jihohi 18, inda Legas kadai ke da mutane 139, sai Kano da Oyo masu mutane 28 kowannensu, yayinda Edo ke da 25, Katsina mutane 22.

A sauran jihohin kuma sabbin mutane 18 suka kamu da coronavirus a Kaduna, Jigawa da Yobe na da 14-14, sai Filato da Yobe masu 13-13, Abuja na da 11, Gombe 8, Ondo 5, sai kuma mutum guda-guda a Rivers da Adamawa.

Zuwa yanz jumillar mutane dubu 1 da 907 suka warke daga cikin dubu 7 da 16 da suka kamu da cutar ta coronavirus a Najeriya, yayinda 211 suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI