Duniya

Halin da ake ciki dangane da karamar Sallah a bana

Wani mutum yayin kokari ganin sabon wata da taimakon na'urar zamani.
Wani mutum yayin kokari ganin sabon wata da taimakon na'urar zamani. Reuters

Ranar Asabar wani bangare na al’ummar Musulmi suka yi bikin karamar Sallah a Jamhuriyar Nijar, kamar yadda abin yake a wasu sassan duniya inda hukumomi suka sanar da karewar Azumin Ramadana.

Talla

A ranar Juma’ar da ta gabata majalisar koli ta malaman addinin Musulunci a kasar ta Nijar, ta sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a garuruwan Magarya, Zindar da kuma yankin Diffa, abinda ke nufin karewar watan Azumin na bana.

Sai dai kamar yadda ya kan faru a wasu lokutan, a shekarar bana ma rahotanni sun nuna cewar an samu sabani kan ganin sabon watan Shawwal, domin kuwa a yayinda ya take ranar Sallah a Jamhuriyar Nijar, a Najeriya mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya ce za a cika kwanaki 30 na Azumin Ramadana saboda rashin samun rahoton ganin sabon wata a fadin kasar, dan haka ya sanar da Lahadi, 24 ga watan Mayu a matsayin ranar Idi wato 1 ga watan Shawwal.

Sanarwar mai alfarma Sultan ta zo ne yayinda wasu malaman addinin Musulunci a Najeriyar ciki har da Shiekh Dahiru Usman Bauchi, suka bayyana ganin sabon watan Shawwal, bayan samun sahihan bayanai daga wasu sassan kasar da ma garuruwan da suke, abinda ya sanya wasu ajiye Azumin da suka dauka da nufin cika kwanaki 30, yayinda wasu ma tun a ranar Juma’a suka daura niyyar yin Sallar Idi a wannan Asabar.

Cikin bayanin da yayi, Shiekh Dahiru Usman Bauchi ya ce bisa ga koyarwar addinin Musulunci ana soma Azumin Ramadana ne ko ajiye shi, idan aka samu rahoton ganin sabon wata daga mutane adalai guda biyu ko kuma daga tawagar jama’ar da ta kunshi akalla mutane 5 baligai masu hankali, abinda ya tabbata a lokacin da Manzon Allah, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam ke raye.

Rahotanni dai sun ce an ga sabon watan Shawwal a wasu yankuna dake Bauchi, Zamfara da kuma Gaidam a Yobe.

A Saudiya kuwa, a ranar Juma’a, 22 ga watan Mayu, majalisar koli ta malaman addinin Musulunci a kasar ta bayyana cewar za a cika kwanaki 30 na watan Ramadan saboda rashin ganin jinjirin watan Shawwal.

Sai dai tuni al’ummar Musulmi suka yi bikin karamar Sallah a wasu kasashen Afrika ciki harda Kamaru, Chadi da kuma Jamhuriyar Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.