Najeriya

Sama da mutane dubu 2 sun warke daga cutar coronavirus a Najeriya

Wasu 'yan Najeriya yayin jiran yi musu gwajin cutar coronavirus a Abuja.  15/4/2020.
Wasu 'yan Najeriya yayin jiran yi musu gwajin cutar coronavirus a Abuja. 15/4/2020. AFP

Cibiyar yaki da yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC tace adadin mutanen da suka warke daga cutar coronavirus a kasar ya kai dubu 2,007, bayan gwajin da aka yi musu har kashi 2 ya tabbatar da cewar basa dauke da cutar.

Talla

Cikin rahoton da ta fitar a ranar Juma’a 22 ga watan Mayu, cibiyar ta NCDC ta ce an samu karin mutane 245 da suka kamu da coronavirus, abinda ya sanya jumillar yawan wadanda suka kamu da cutar a Najeriya kaiwa dubu 7 da 261.

Cibiyar yaki da yaduwar cutukan ta Najeriya ta yi karin bayanin cewa, zuwa yanzu ta samu nasarar yiwa ‘yan Najeriyar akalla dubu 41 da 907 gwajin cutar coronavirus, daga cikin dubu 7 da 261 da suka kamu kuma jumillar mutane 221 sun mutu.

Yanzu haka dai annobar coronavirus ta halaka akalla mutane dubu 335 da 538 a fadin duniya, daga cikin miliyan 5 da 158 da 750 da suka kamu da cutar a kasashe kusan 200, yayinda wasu miliyan 1 da dubu 937 da 200 suka warke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.