Najeriya

Sojin Najeriya sun halaka 'yan bindiga 135 a Zamfara da Katsina

Wasu dakarun rundunar sojin Najeriya.
Wasu dakarun rundunar sojin Najeriya. AFP / Audu Marte

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da samun nasarar halaka ‘yan bindiga akalla 135, yayin farmakin da ta kaddamar kansu a yankunan dake tsakanin jihohin Zamfara da Katsina.

Talla

Kakakin rundunar sojin Najeriyar Manjo Janar John Enenche, yace an kaddamar da samame kan ‘yan bingidar ne da jiragen yaki, a tsakanin ranakun 20 zuwa 22 ga watan Mayu.

Manjo Janar Enenche ya kuma ce bayaga halaka tarin ‘yan bindigar, dakarun sojin sun lalata sansanonin maharan da dama a tsakanin dazukan dake kananan hukumomin Jibia, da DanMusa a Katsina, sai kuma Birnin Magaji da Zurmi a jihar Zamfara.

A shekarun baya bayan nan yankuna da dama a jihohin Zamfara, Katsina da kuma wasu yankunan Sokoto na fuskantar hare-haren ‘yan bindiga dake halaka mutane gami da sace su don karbar kudin fansa, bayaga cin zarafin mata da kuma satar dukiya ciki harda dabbobi.

Tsanantar matsalar rashin tsaron ce kuma ta tilastawa dubban ‘yan Najeriya tserewa daga muhallansu zuwa kauyukan Jamhuriyar Nijar dake kan iyaka.

Sai dai a baya bayan nan hukumomin na Nijar suka suka koka kan yadda gungun ‘yan bindigar daga Najeriya ke tsallakawa cikin kasar tare da kai farmaki kan wasu kauyukan dake karbar bakuncin ‘yan gudun hijirar da suka raba da muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.