Najeriya

'Yan sanda sun kama fitaccen malami bisa tuhumarsa da cin zarafin El-Rufa'i

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i.
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i. The Nation

Rahotanni daga Najeriya sun ce jami’an tsaro sun kama Malam Bello Yabo, fitaccen malamin addinin Islama dake jihar Sokoto, bisa tuhumarsa da furta kalaman batanci kan gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i.

Talla

Yayin zantawa da jaridar Daily Trust dake Najeriya, malam Abdullahi Abubakar Yabo, dan uwa ga fitaccen malamin, yace an kama yayan nasa ne da yammacin ranar Juma’ar nan da ta gabata, inda suka wuce da shi zuwa Kaduna.

Malam Abdullahi Abubakar yace bayan kammala Sallar La’asar ne jami’an ‘yan sanda sanye da farin kanya suka bukaci ganawa da malam Bello Yabo, inda suka nuna masa takardar da wata kotun Majistre a Kaduna ta bada na umarnin gurfanar da shi gabanta bayan bikin Sallah karama.

Ana kyautata zaton cewa kamen da aka yiwa fitaccen malamin na da alaka da wani bidiyo wanda a cikinsa yake caccakar sukar El-Rufa’i kan matakinsa na cigaba hana Sallar Juma’a da kuma Idi, tare da sukar majalisar malaman jihar Kaduna bisa yadda yace sun kyale gwamnan yana juya su yadda ya so.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.