Najeriya-Coronavirus

Matakan killace jama'a ba za su cigaba da wanzuwa tsawon lokaci ba - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Solacebase

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shaidawa ‘yan kasar cewa, matakan killace su da kuma takaita zirga-zirga da suka gurgunta lamurran yau da kullum saboda annobar coronavirus, ba za su cigaba da wanzuwa na lokaci mai tsawo a nan gaba ba.

Talla

Shugaban ya ce gwamnati na bibiyar halin da ake ciki kan matakan yaki da cutar, kuma za a cigaba da sassautawa, da ma janye matakan idan lokaci yayi.

Cikin sakon taya murnar zagayowar Sallah karama da ya aikewa ‘yan Najeriya ta hannun kakakinsa malam Garba Shehu, Buhari ya taya jama’a alhinin yadda annobar coronavirus ta yi tasiri wajen sauya yanayin Ibada, zamantakewa da kuma durkusar da tattalin arzikin kasar.

Sai dai shugaban ya bukaci ‘yan Najeriya da su cigaba da nuna juriya gami da fata mai kyau, da kuma bin dokokin gwamnati da sharuddan kwararru a fannin lafiya, domin gaggauta ganin bayan annobar ta coronavirus.

Yau Lahadi mafi akasarin al'ummar Musulmi a Najeriya ke bikin Sallar Idi karama bayan cika kwanaki 30 na watan Azumin Ramadana, biyo bayan rashin ganin jinjirin watan Shawwal da mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Abubakar Sa'ad III ya sanar, inda ya bayyana yau a matsayin ranar Idi.

Sai dai tun a ranar Asabar wasu daga cikin al'ummar Musulmin suka gudanar da Sallar tasu bisa hujjar ganin sabon wata a wasu garuruwan Najeriya da suka hada da Bauchi, Zamfara da kuma Yobe, bayaga samun rahoton ganin watan na Shawwal a Jamhuriyar Nijar a daren ranar Juma'ar da ta gabata, abinda ya sanya wasu ajiye azumin watan na Ramadana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI