Najeriya-Borno

Sojin Najeriya sun halaka mayakan Boko Haram sama da dubu 1 - Buratai

Wasu daga cikin dakarun rundunar sojin Najeriya.
Wasu daga cikin dakarun rundunar sojin Najeriya. Getty Images

Babban Hafsan Sojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai yace dakarun kasar a sun yi nasarar halaka mayakan Boko Haram dubu 1 da 15, cikin makwanni 6.

Talla

Buratai ya bayyana samun nasarar ce yau lahadi a Maiduguri, yayin taron liyafar da ya shiryawa dakarun rundunar 'Operation lafiya Dole' dake yakar ta’addanci a arewa maso gabashin Najeriya.

Babban hafsan sojin Najeriyar ya ce sun samu gagarumar nasarar ce, bayan kaddamar da sabon farmaki a karkashin jagorancinsa kan mayakan na Boko Haram daga ranar 12 ga watan Afrilun da ya gabata zuwa yanzu.

Buratai ya kara da cewa a tsawon makwanni 6 da suka shafe suna luguden wutar, sun samu nasarar kame manyan ‘ya’yan kungiyar ta Boko Haram 84, da suka hada da kwamandoji, masu yi musu leken asiri, da kuma masu yi musu safarar makamai da sauran kayayyakin bukata.

Shugaban rundunar sojin na Najeriya ya jinjinawa hadin gwiwar rundunar sojin saman kasar, sojin ruwa, ‘yan sanda, jami’an DSS da kuma jami’an tsaron sa kai na Civilian JTF bisa gudunmawar da suka jajirce wajen bayarwa.

Idan za a iya tunawa dai a farkon watan Afrilun da ya gabata na shekarar nan  ta 2020, babban hafsan sojin Najeriyar Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya koma yankin arewa maso gabashi kasar, domin karfafa dakarun dake yakar kungiyar Boko Haram, inda ya sha alwashin kawo karshenta kafin barin fagen dagar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.