Najeriya

Buhari ya bukaci kara yawan abincin da ake nomawa a Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AFP

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci manoman kasar da su kara yawan abincin da suke nomawa, la’akari da cewar a halin da ake ciki, Najeriyar ba ta da kudaden sayen abinci daga kasashen ketare don shigar da shi kasar.

Talla

Shugaba Buhari ya zaburar da manoman ne a Lahadin da ta gabata, jim kadan bayan kammala sallar Idi tare da iyalinsa a Abuja, inda ya taya su fatan samun damina mai albarka.

Bayyana cewar Najeriya ba ta da kudaden sayen abinci daga kasashen ketare da Buhari yayi, na zuwa kwanaki kalilan bayan gargadin da ministar kudin kasar Zainab Ahmed ta yi a makon jiya, inda tace babu makawa sai tattalin arzikin Najeriya ya durkushe nan bada jimawa ba, muddin annobar coronavirus ta cigaba da wanzuwa nan da tsawon lokaci.

Najeriya dai na daga cikin kasashen duniyar da tasirin annobar coronavirus ya fi illata tattalin arzikinsu, la’akari da cewar kusan kaso 90 na kudaden shigar da kasar ke samu daga danyen mai ne, wanda cutar tayi sanadin faduwar farashin gangarsa a kasuwannin duniya daga kusan dala 60 zuwa kasa da dala 20, kafin daga bisani ya koma dala 30 a yanzu.

Zalika matakan killace jama’a da rufe ma’aikatu, da kuma masana’antu saboda dakile yaduwar coronavirus, ya sanya miliyoyin gangunan danyen man da Najeriya ta fitar kafin yaduwar annobar, yin kwantai a kasuwannin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.