Najeriya-Coronavirus

Karin mutane 313 sun kamu da coronavirus a Najeriya

Jami'ar lafiya a Najeriya yayin gwada zafin jikin wata mata.
Jami'ar lafiya a Najeriya yayin gwada zafin jikin wata mata. REUTERS / AFOLABI SOTUNDE

Yawan masu coronavirus a Najeriya ya karu da mutane 313, abinda ya sanya jumillar adadin wadanda suka harbu da cutar a kasar kaiwa dubu 7 da 839, sai dai daga cikinsu mutane dubu 2 da 263 sun warke, yayinda 226 suka rasa rayukansu.

Talla

Cibiyar yaki da yaduwar cutuka a Najeriya NCDC ta wallafa rahoton samun karin mutanen 313 ne a daren ranar Lahadin da ta gabata.

Cibiyar tace Legas ce ke kan gaba da adadin sabbin mutanen da suka kamu 148, sai Abuja mai mutane 36, Rivers 27, Edo na da 19, Kano 13, Ogun 12, sai kuma Edo da sabbin mutane 11 suka kamu da cutar ta coronavirus.

Sauran jihohin sun hada da Nasarawa da Delta wadanda dukkaninsu ke da karin mutane 8 da suka kamu, Oyo na da mutane 7, Filato mutane 6, Kaduna 5, sai kuma mutane 4 a Kwara. Akwa Ibom da Bayelsa na da mutane 3-3, Niger na da mutane 2, sai Anambra mai mutum 1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.