Najeriya

Jiragen yakin Najeriya na cigaba da luguden wuta kan 'yan bindiga a Zamfara da Katsina

Daya daga cikin zaratan sojin Najeriya yayin dira daga jirgin yaki mai saukar Ungulu. (An yi amfani da wannan hoto a matsayin misali)
Daya daga cikin zaratan sojin Najeriya yayin dira daga jirgin yaki mai saukar Ungulu. (An yi amfani da wannan hoto a matsayin misali) AFP PHOTO / STEFAN HEUNIS

Bayanai dake fitowa daga yankin arewa maso yammacin Najeriya sun ce dakarun sojin Najeriya na ci gaba da ruwan wuta kan 'yan bindiga da a ‘yan kwanakin nan ke kai hare-hare kan mazauna wasu kauyukan jihohin Katsina da Zamfara.

Talla

Tuni dai dakarun sojin suka lalata sansanonin 'yan bindigar da dama a tsakanin dazukan dake kananan hukumomin Jibia a Katsina, sai kuma Zurmi a jihar Zamfara.

A cikin wannan rahoto da Faruk Mohammad Yabo ya aiko mana daga Sokoto, za a ji yadda mazauna kauyukan dake kusa da inda ake dauki-ba-dadin ke bayyana yadda ‘yan bindigar ke tserewa.

Rahoto kan yadda jiragen yakin Najeriya ke luguden wuta kan 'yan bindiga a Zamfara da Katsina

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.