Najeriya

Kungiyar manoma ta maida martani kan umarnin Buhari na wadata Najeriya da abinci

Watan kafatariyar gona a garin Jere dake jihar Kaduna. 10/10/2018.
Watan kafatariyar gona a garin Jere dake jihar Kaduna. 10/10/2018. REUTERS/Afolabi Sotunde

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bukaci manoman kasar da su kara azama don wadatar da kasar da abinci, saboda a cewarsa Najeriya ba ta da kudin da za ta yi amfani da su domin sayo abinci daga ketare.

Talla

Sai dai sakataren yada labaran kungiyar manoman Najeriya, Alhaji Muhammad Magaji, ya ce akwai abubuwan da ya kamata gwamnati ta yi domin ganin cewa manoma sun wadatar da kasar da abinci.

Yayin zantawa da sashin Hausa RFI, Alhaji Magaji ya bayyana rashin kai kayayyakin tallafi ga manoma musamman taki, zuwa sassan Najeriya a halin yanzu, saboda matakan takaita zirga-zirga tsakanin jihohi dake aiki saboda annobar coronavirus, duk da cewa dokar hana zirga-zirgar ba ta shafi masu ayyukan na musamman ba, ciki har da na noma.

Sakataren yada labaran kungiyar manoman Najeriya, Alhaji Muhammad Magaji kan umarnin Buhari na wadata kasar da abinci

Wani batu dake ciwa manoma da sauran jama’a tuwo a kwarya kuma shi ne tsaro, la’akari da cewar hare-haren ‘yan bindiga dake halakawa da satar jama’a don karbar kudin fansa ya gurgunta ayyukan gona a arewacin Najeriya, musamman a jihohin Zamfara, Katsina, Kaduna da kuma wasu yankunan jihar Sokoto, inda manoma ke fargabar zuwa gonakinsu, gudun abinda ka iya biyo baya.

Bayyana cewar Najeriya ba ta da kudaden sayen abinci daga kasashen ketare da Buhari yayi, na zuwa kwanaki kalilan bayan gargadin da ministar kudin kasar Zainab Ahmed ta yi a makon jiya, inda tace babu makawa sai tattalin arzikin Najeriya ya durkushe nan bada jimawa ba, muddin annobar coronavirus ta cigaba da wanzuwa nan da tsawon lokaci.

Najeriya dai na daga cikin kasashen duniyar da tasirin annobar coronavirus ya fi illata tattalin arzikinsu, la’akari da cewar kusan kaso 90 na kudaden shigar da kasar ke samu daga danyen mai ne, wanda cutar tayi sanadin faduwar farashin gangarsa a kasuwannin duniya daga kusan dala 60 zuwa kasa da dala 20, kafin daga bisani ya koma dala 30 a yanzu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI