Najeriya-Kaduna

Za mu daure duk wanda muka samu da laifin tura yara almajiranci - El-Rufa'i

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i.
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i. kdsg.gov.ng

Gwamnan Kaduna malam Nasir El-Rufa’i ya sha alwashin daukar tsattsauran mataki na daurin gidan Yari ko tilasta biyan tara mai kauri, kan wanda duk aka samu da laifin shigar da dansa ko wanda ke karkashinsa cikin tsarin karatun almajiranci.

Talla

El-Rufa’i ya ce ga malamai kuwa, duk wanda aka samu da laifin sanya yaro a almajirancin za su fuskanci hukuncin dauri da kuma biyan tarar da ka iya kamawa daga naira dubu 100 zuwa dubu 200 kan kowane yaro dake karkashin malami.

Wakilinmu dake Kaduna ya ce gwamnan yayi gargadin ne, a lokacin da yake ziyartar wasu almajirai ‘yan asalin jihar kimanin 200 da gwamnatin jihar Nasarawa ta maida gida.

El-Rufa’i yace almajiran da aka sauke su a makarantar sakandaren Kurmin Mashi, da ma saura dake tafe daga wasu jihohin, za su samu kulawar gwamnatin Kaduna.

A farkon watan Mayu, gwamnan Kaduna ya sanar da kawo karshen tsarin karatun Almajirci a daukacin jihar, matakin da yace gwamnonin arewacin Najeriya suka cimma matsayar dauka.

El Rufa’i ya kuma ce tuni nazari yayi nisa kan samar da waso dokoki tabbatar da cewa, tsarin karatun na almajirci bai sake farfadowa ba a jihar.

Tuni dai gwamnatin Kaduna ta maida almajirai akalla dubu 30 zuwa jihohinsu na asali, akmar yadda gwamnan jihar ya tabbatar yayin wata zantawa da gidan talabijin na Channels TV dake Najeriya a farkon watan Mayu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.