El-Rufa'i ya sake tsawaita dokar kulle a Kaduna
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Gwamnan Kaduna a Najeriya, Malam Nasir El-Rufa’I ya kara wa’adin dokar killace al’ummar jihar da tsawon mako 2, domin karfafa yakar annobar coronavirus.
Tsawaita wa’adin dai na zuwa ne yayinda al’ummar jihar ta Kaduna ke shirin cika kwanaki 60 suna karkashin dokar kullen da aka kafa domin dakile yaduwar cutar ta coronavirus.
Yayin sanar da matakin ta hannun mataimakiyarsa, dakta Hadiza Balarabe, El-Rufa’i yace sabuwar dokar hana fitar za ta soma aiki ne daga ranar 1 ga watan Yuni mai kamawa, bayan karewar wadda ke aiki a yanzu.
Sanarwar ta ce gwamnati za ta cigaba da sassaucin baiwa jama’a damar fita a ranakun Laraba da kuma Alhamis, amma da zarar sabon wa’adin kullen ya soma aiki, daga farkon watan Yuni, za a rika baiwa mutane damar fita harkokin yau da kullum ne a ranakun Alhamis, Laraba da kuma Talata.
Hadiza Balarabe, mataimakiyar gwamnan jihar ta Kaduna, ta ce an dauki wannan mataki ne domin cigaba da baiwa al’ummar jihar kariya da annobar ta coronavirus ko COVID-19.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu