Najeriya-Amnesty

Yara na cikin halin 'rana zafi inuwa kuna' a arewa maso gabashin Najeriya - Amnesty

Wata yarinya dauke da ruwan sha, yayinda mata da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu, suka yi layi don karbar bargunan rufa daga sojojin Najeriya a garin Damasak dake Borno. 24/3/2015.
Wata yarinya dauke da ruwan sha, yayinda mata da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu, suka yi layi don karbar bargunan rufa daga sojojin Najeriya a garin Damasak dake Borno. 24/3/2015. REUTERS/Joe Penney

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International, a yau laraba ta fitar da wani sabon rahoto a dake bayyana mawuyacin halin da yara kanana ke ciki a jihohin Borno da Adamawa.

Talla

Cikin sabon rahoton Amnesty ta ce ana tursasawa kananan yaran, mata da maza auren dole da kuma zama mayakan kungiyar Boko Haram.

Har ila yau rahoton ya yi zargin cewa idan yaran sun kubuta zuwa hannun jami’an tsaro, a can ma ana gallaza musu da kuma tsare su ba bisa ka’ida ba.

Wakilin mu na Abuja Muhammad Sani Abubakar ya hada mana rahoto kan wannan al'amari.

Kananan yara na cikin mawuyacin hali a arewa maso gabashin Najeriya - Amnesty

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI