Najeriya

Najeriya na bukatar karin gadajen kwantar da masu cutar coronavirus - Mustapha

Sabuwar cibiyar kula da masu cutar coronavirus dake filin wasa na Mobolaji Johnson Arena a jihar Legas dake Najeriya. 27/3/2020.
Sabuwar cibiyar kula da masu cutar coronavirus dake filin wasa na Mobolaji Johnson Arena a jihar Legas dake Najeriya. 27/3/2020. REUTERS/Temilade Adelaja

Sakataren gwamnatin Najeriya kuma shugaban kwamitin yaki da annobar coronavirus a kasar Boss Mustapha, yayi gargadin cewa fannin lafiya na fuskantar gagarumin kalubale, la’akari da adadin masu cutar coronavirus dake cigaba da karuwa.

Talla

Yayin taron manema labarai da ya saba jagoranta kan halin da ake ciki dangane da yakar annobar, Boss Mustapha yace a daidai lokacin da yawan masu cutar ya haura dubu 5, kasar na fuskantar karancin gadajen kwantar da marasa lafiyar a jihohi da dama.

A cewar shugaban kwamitin yakar cutar, akalla jihohin Najeriya 21, na da gadajen kwantar da masu cutar coronavirus kasa da 100 a yanzu haka, abinda ke zama babbar barazana, idan aka cigaba da fuskantar hauhawar wadanda ke kamuwa da cutar.

Sai dai sakataren gwamnatin Najeriyar yace a yanzu haka bayan ganawa da wani adadi na kwararrun masu magani, gwamnati ta zabi wasu magungunan gargajiya 3 da ta baiwa kwararrunta damar gudanar da bincike akansu a kokarinta na laluben maganin cutar ta coronavirus.

Kwamitin yaki da annobar ta coronavirus ya kuma gargadi hukumomi, jami’an lafiya, da kuma daidakun mutane kan amfani da maganin Hydroxychloroquine don warakarwa ko samun kariya daga cutar, bayanda da hukumar lafiya ta duniya WHO ta bada umarnin dakatar da gwajinsa, saboda binciken wasu kwararru da suka ce yana tattare da matsalar kara sabubban mutuwar marasa lafiya dake fama da coronavirus.

Sai dai a nata bangaren hukumar tantance ingancin magunguna da abinci ta Najeriya NAFDAC, ta ce gwajin maganin na Hydroxychloroquine zai cigaba, domin kuwa nata bayanan kwararrun sun nuna cewar yana tasiri wajen warakar da masu cutar ta coronavirus, musamman wadanda ba ta yiwa mugun kamu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.