Tattaunawa kan dalilan da suka hana gyara hanyoyin Najeriya tare da Alhaji Shehu Ashaka

Sauti 03:33
Yadda wata babbar hanya ta lalace a jihar Edo dake Najeriya
Yadda wata babbar hanya ta lalace a jihar Edo dake Najeriya The Guardian Nigeria

A Najeriya lalacewar hanyoyin na ci gaba da haddasa asarar dubban rayuka da tarin dukiya sakamakon munanan hadurran da ke ci gaba da faruwa, baya ga ta’azzarar ayyukan garkuwa da mutane da kuma fashi da makami wadannan dukka ke da nasaba da lalacewar hanyoyin.Duk da wadannan matsaloli dai za a iya cewa mahukuntan Najeriya sun gaza gyara hanyoyin tsawon shekaru, duk kuwa da ikirarin gwamnatoci na magance matsalar na yanzu da wadanda suka gabata.Alhaji Shehu Ashaka wani dattijo a Najeriyar ya yi mana tsokaci kan dalilan da ya ke ganin sun hana gyaran hanyoyin yayin tattaunawarsa da Abubakar Isa Dandago.