Najeriya

Buhari ya gabatarwa majalisa bukatar neman bashin dala biliyan 5.5

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. © Nigeria Presidency/Handout via REUTERS

Rahotanni daga Najeriya sun ce shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya gabatarwa da zauren majalisar dokoki bukatar karbar karin bashin dala biliyan 5, da miliyan 513 daga kasashen ketare.

Talla

Bayanai sun ce koda yake basu kai ga amincewa da bukatar kai tsaye ba, bayan nazari kan batun, wasu ‘yan majalisar dattijai sun cimma matsayar cewa ba laifi bane karbo karin bashin, zalika ba zai zamewa Najeriya matsala ba.

Kafin gabatar da sabuwar bukatar karbar bashin a farkon shekarar nan majalisar dattijan Najeriya ta amince da bukatar gwamnati na nemo bashin dala biliyan 22.79 domin cike gibin kasafin kudin kasar na bana da ya kai naira triliyan 10 da rabi.

Zalika cikin watan Afrilun da ya gabata zauren majalisar dokokin Najeriya ya amincewa gwamnatin tarayyar kasar karbar bashin naira biliyan 850, sai dai za a karbi bashin ne a cikin gida.

A cikin watan nan na Mayu Ministar kudin Najeriya Zainab Ahmed tace babu makawa sai tattalin arzikin Najeriya ya durkushe nan bada jimawa ba, muddin annobar coronavirus ta cigaba da wanzuwa nan da tsawon lokaci.

Najeriya dai na daga cikin kasashen duniyar da tasirin annobar coronavirus ya fi illata tattalin arzikinsu, la’akari da cewar kusan kaso 90 na kudaden shigar da kasar ke samu daga danyen mai ne, wanda cutar tayi sanadin faduwar farashin gangarsa a kasuwannin duniya daga kusan dala 60 zuwa kasa da dala 20, kafin daga bisani ya koma dala 30 a yanzu.

Zalika matakan killace jama’a da rufe ma’aikatu, da kuma masana’antu saboda dakile yaduwar coronavirus, ya sanya miliyoyin gangunan danyen man da Najeriya ta fitar kafin yaduwar annobar, yin kwantai a kasuwannin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.