Najeriya-Coronavirus

Gwamnatin Kogi ta yi watsi da rahoton bullar annobar coronavirus a cikinta

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello.
Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello. Twitter/@GovernorBello

Gwamnatin Kogi ta yi watsi da rahoton bullar annobar coronavirus cikin jihar, wanda a ranar Laraba 27 ga watan Mayu, cibiyar yaki da yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC ta bayyana samun mutane 2 da suka kamu da cutar.

Talla

A rahoton na ranar Laraba, NCDC tace an samu karin mutane 389 da suka kamu da coronavirus a Najeriya, a tsakanin jihohin kasar 22, ciki harda Kogi, wadda a baya annobar bata bulla cikinta.

Wannan ta sanya cibiyar yaki da cutukan tabbatar da cewar, jihar Cross-River ce kawai ta rage a Najeriya da annobar coronavirus bata bulla cikinta ba.

Sai dai kwamishinan lafiyar jihar ta Kogi Haruna Audu, yace gwamnati ba za ta amince da kirkirarren labarin da cibiyar NCDC ta Najeriya ta yada kansu ba, inda kwashinan ya nanata matsyin gwamnatin jihar Kogin na cewa har aynzu babu annoba ko cutar coronavirus a jihar.

Dangane da mutane biyun da cibiyar NCDC tace sun kamu da coronavirus kuwa, gwamnatin Kogi ta ce mutum na farko limamin wani Masallaci da kudan zuma ya ciza, amma bayan yi masa gwaji a cibiyar kula da lafiya ta gwamnatin Najeriya dake Lokoja, sai aka ce wai ya kamu da cutar ta coronavirus, yayinda kuma daya mutumin aka kaishi asibiti dauke da wasu alamun cutar, bayan sa’o’i 24 da gwajin ne kuma shi ma aka ce ya harbu da cutar.

An dai share makwanni ana takkadama tsakanin cibiyar yaki da cutuka a Najeriya NCDC da gwamnatin Kogi, inda cibiyar ke gargadin jihar da ta kaucewa tafka kuskuren da zai yi sanadin salwantar dubban rayuka jama’a bayan ikirarin babu annobar coronavirus a cikinta gami da korar tawagar jami’anta, yayinda shi kuma gwamnan Kogi Yahaya Bello ke cigaba da nanata cewar babu mai dauki da cutar a jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.