Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta bayyana yadda za ta kasafta kudaden marigayi Abacha

Dalar Amurka.
Dalar Amurka. Reuters

Gwamnatin Najeriya ta sanar da yadda za ta kashe kudaden tsohon shugaban kasar marigayi Janar Sani Abacha da aka karbo daga Tsibirin Jerssey.

Talla

‘Yan Najeriya da dama sun jima suna saurare domin jin yadda gwamnatin kasar za ta tafiyar da Kudaden da suka haura dala milyan 300,

Ga rahoton Muhammad Sani Abubakar daga Abuja.

Gwamnatin Najeriya ta bayyana yadda za ta kasafta kudaden marigayi Abacha

A farkon watan Mayu nan gwamnatin Amurka ta sanar da gano wasu sabbin makudan kudade na dala miliyan 319, kwatankwacin naira biliyan 121, da Amurkan tace tsohon shugaban Najeriya, marigayi Janar Sani Abacha ya boye a kasashen Birtaniya da kuma Faransa.

Cikin sanarwar da ya fitar, ofishin jakadancin Amurka a Najeriya yace dala miliyan 167 na boye a Faransa, yayinda dala miliyan 152 ke Birtaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.