Najeriya

'Yan bindiga sun halaka mutane 15 a wasu kauyukan Katsina

Hoton 'yan bindiga (domin misali kawai )
Hoton 'yan bindiga (domin misali kawai ) Jakarta Globe

Rahotanni daga jihar Katsina a Najeriya sun ce ‘yan bindiga sun halaka akalla mutane 15, a wani sabon farmaki da suka kai kan wasu kauyukan kananan hukumomin Faskari da Sabuwa.

Talla

Shaidun gani da ido sun ce, ‘yan bindigar sun kai sabon farmakin ne kan garuruwan Maigora, Unguwar Gizo, Mai Ruwa da kuma sabon Layin galadima dake karamar hukumar Faskari, sai kuma Machika dake karamar hukumar Sabuwa.

Majiyoyin sun kara da cewar cikin tsakar daren ranar Alhamis ‘yan bindigar suka afkawa kauyukan, suka kuma cigaba da yin ta’adi har zuwa wayewar garin yau Juma’a.

Bayanai sun bayyana kokarin da mazauna yankunan da aka kaiwa harin suka yi na maidawa ‘yan bindigar raddi ne ya janyo hasarar rayukan mutanen 15, bayaga sace dabbobi da dama, sai dai yayin tabbatar da rahoton kai farmakin, rundunar ‘yan sandan Katsina ta bakin kakakinta SP Gambo Isah, tace mutane 13 suka rasa rayukansu ba 15 ba.

Sabon farmakin na zuwa ne bayan jerin hare-haren da gungun ‘yan bindiga suka kai kan wasu kauyukan karamar hukumar Sabon Birni dake jihar Sokoto a ranar Laraba, 27 ga watan Mayu, inda suka kashe akalla mutane 70.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.