Najeriya-Coronavirus

Yawan wadanda suka kamu da cutar corona a Najeriya ya haura dubu 9

Wani jami'in lafiya a Najeriya, yayin gwajin cutar coronavirus a birnin Abuja. Afrilu, 2020.
Wani jami'in lafiya a Najeriya, yayin gwajin cutar coronavirus a birnin Abuja. Afrilu, 2020. REUTERS/Afolabi Sotunde

Yawan wadanda suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya kai dubu 9 da 302, bayan da cibiyar yaki da yaduwar cutuka ta kasar NCDC ta bayyana samun karin mutane 387 da suka kamu da cutar a daren jiya Juma’a 29 ga watan Mayu.

Talla

Rahoton cibiyar ta NCDC yace a wannan karon an samu sabbin mutanen da suka kamu da cutar at coronavirus a jihohi 13 da birnin Abuja, kuma Legas ke kan gaba wajen yawan wadanda da cutar ta kama da adadin mutane 254.

Sauran jihohin sun hada da Abuja mai mutane 29, Jigawa 24, Edo 22, Oyo 15, Rivers 14, Kaduna 11, Borno 6, Kano 3, Filato, Yobe, Gombe da kuma Bauchi dukkaninsu mutane 2-2, sai kuma Ondo mai mutum guda.

Zuwa yanzu jumillar mutane dubu 2 da 697 suka warke daga cikin dubu dubu 9 da 302 da suka kamu da coronavirus a Najeriya, daga cikinsu kuma 261 sun mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI