Najeriya

Ba za mu bude Masallatai da Coci ba-gwamnatin Lagos

Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, tare da mataimakinsa Obafemi Hamzat daga hadu, sai kuma kwamishinansa na lafiya Farfesa Akin Abayomi.
Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, tare da mataimakinsa Obafemi Hamzat daga hadu, sai kuma kwamishinansa na lafiya Farfesa Akin Abayomi. LASG

Gwamnatin jihar Lagos da ke kudancin Najeriya ta ce, ba za ta gaggauta bude Masallatai da Coci-coci ba ga masu ibada a jihar.

Talla

Kwamishinan Cikin Gida, Prince Anofiu Elegushi ya bayyana haka a gefen taron bitar cika shekara guda da gwamnann jihar Babajide Sanwo-Olu ya yi a kan karaga.

Elegushi ya ce, har yanzu Lagos ce cibiyar annobar coronavirus, a don haka babu yadda za a bude wuraren ibada cikin hanzari.

Tun a ranar Litinin gwamnatin tarayya ta janye dokar hana taruwar ibada a Masallatai da Majami’u a fadin Najeriya, amma ta ce, aiwatar da matakin ya ta’allaka da sharuddan da gwamnoni jihohi suka amince da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI