Najeriya

Za a koma ibada a Masallatai da Majami'u na Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Nigeria Presidency/Handout via REUTERS

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana shirinta na sassauta dokar hana taruwar idaba a Masallatai da Majami’u wadda ta kafa don hana bazuwar cutar coronavirus, yayin da ta rage sa'o'in dakatar da zirga-zirga da a kalla awa hudu.

Talla

Kwamitin Shugaban Kasa da ke Yaki da Covid-19 ya ce, sassauta dokar hana taruwar ibadar, ta ta'allaka da wasu ka'idoji da gwamnatocin jihohin Najeriya suka amince da su.

Shugaban Kwamitin Yaki a cutar, Boss Mustapha ya ce, za a fitar da sharudda kan yadda za a koma gudanar da ibada a Masallatan da Majami'un.

Sai dai har yanzu akwai dokar hana taruwar mutanen da adadinsu ya zarta 20, yayin da dokar haramcin balaguro tsakanin jihohin kasar za ta ci gaba da aiki.

Yanzu haka jama’a na da damar zirga-zirga a cikin jihohinsu tun daga karfe na 4 na asuba zuwa 10 na dare, sabanin dokar da aka kafa a can baya, wadda ta takaita zirga-zirgar daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe.

Bayanai na cewa, gwamnatin tarayya ta amince ta sake bude Masallatai da Majami’u ne bayan shugabannin addinai na kasar sun matsa lamba, lura da cewa, an bai wa jama’a damar ci gaba da harkokinsu a kasuwanni amma wuraren ibada suka ci gaba da kasancewa a rufe, matakin da suka ce ya saba hankali.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da adadin mutanen da suka harbu da kwayar cutar coronavirus a Najeriya ya zarta dubu 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI