Najeriya

Abin da ya faru bayan auren Hameed Ali a Kano

Mutumin da shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya Kanar Hameed Ali ya kasa a neman aure a ‘yan kwanakin nan a jihar Kano, ya musanta cewa, yana da masaniya kan wata takardar wasika da aka yada a kafafen labarai da ke neman a biya shi daukacin kudaden da ya kashe wa amaryar.

Hameed Ali tare da sabuwar amaryarsa Zainab Yahya
Hameed Ali tare da sabuwar amaryarsa Zainab Yahya RFI Hausa/Dandago
Talla

Zabairu Dalhatu Malami ya ce, ba da yawunsa aka fitar da wannan wasika ba da ke neman a biya shi Naira milyan 9.

A ranar Litinin takardar wasikar ta karade kafafen sada zumunta, inda ta yi bayai dalla-dalla kan kudaden da aka ce Malami ya kashe wa Zainab Yahya kafin shugaban kwastam din ya kasa shi.

A cikin sabuwar sanarwar da ya fitar da ke musanta ikirarin farko, Malami ya ce “ Ni Zubairu Malami mazaunin lamba 224 unguwar Durimin Zungura a jihar Kano, ina sanar da jama’a cewa takardar da aka wallafa a Sahara Reporters da sauran kafafen yada labarai, ba da yawuna aka fitar ba.

« Zainab ta kasance wadda na nemi aurenta amma Allah bai nufa ba, don haka ina mata fatan alkhairi da fatan zuriya dayyiba”

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI