Najeriya

Akwai bukatar daukar matasa dubu 100 aikin soja a Najeriya

Kwamitin Kula da Aikin Soji a Majalisar Wakilan Najeriya, ya bukaci gwamnatin kasar ta kaddamar da aikin dibar sabbin sojoji a kalla dubu 100 daya domin tunkarar matsalolin tsaro da kasar ke fama da su da suka hada da rikicin Boko Haram.

Rundunar sojin Najeriya na fama da karancin jami'an tsaro da kayayyakin aiki
Rundunar sojin Najeriya na fama da karancin jami'an tsaro da kayayyakin aiki AFP / Audu Marte
Talla

Kwamitin wanda ya gudanar da bincike a game da yawaitar hare-haren da ‘yan boko haram ke kai wa a kan hanyar da ta hada Maiduguri da Damaturu, ya gano cewa babbar matsalar ita ce karancin sojoji da kuma rashin kayan aiki.

A yayin zantawarsa da sashen Hausa na RFI, shugaban kwamitin Hon. Abdurrazak Namdas ya bayyana cewa, Najeriya na fama da matsalar karancin sojoji, a don haka akwai bukatar shigar da dubban matasa cikin aikin na soji.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirar da Abdulkarim Ibrahim Shikal ya yi da Namdaz kan wannan batu.

Hon. Namdaz kan batun dibar matasa dubu 100 aikin soja a Najeriya

Baya ga rikicin Boko Haram, Najeriya na fama da matsalar 'yan bindiga da ke kashe jama'a babu kakkautawa da kuma masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.

Da ma dai masana lamurran tsaro sun sha fadin cewa, Najeriya na fama da karancin jami'an tsaro, lamarin da ya kasance daya daga cikin dalilan gazawa wajen kawo karshen ta'addanci da tabbatar da cikekken tsaro

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI