Najeriya

An cafke kattan da suka yi wa yarinya fyade a Jigawa

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce, ta cafke mutane 11 da suka yi wa wata yarinya ‘yar shekara 12 fyade a Kasuwar Limawar garin Dutsen Jihar Jigawa ciki kuwa har da wani mutum dan shekaru 57, yayin da hukumar ta ce, ta baza komarta wajen neman wasu wadanda suka yi wa wata ‘yar makaranta mai suna Vera Uwaila a jihar Edo fyaden da yayi sanadiyar mutuwarta.

Matsalar fyade ta zaman ruwan dare game duniya a Najeriya
Matsalar fyade ta zaman ruwan dare game duniya a Najeriya Daily Trsut
Talla

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakken rahoton Muhammad Kabiru Yusuf daga birnin Abuja.

An cafke kattan da suka yi wa yarinya fyade a Jigawa

Kungiyoyin Kare Hakkin Mata sun sha bukatar yanke hukuncin kisa kan duk balagaggen da aka samu da laifin yi wa karamar yarinya fyade a Najeriya.

Wannan matsalar ta zama ruwan dare game duniya a Najeriya da wasu kasashen Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI