Najeriya

Gwamnan Borno ya kori ma'aikatan asibiti saboda sakaci

Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum.
Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum. RFI Hausa / Ahmad Abba

Gwamnan Jihar Bornon Najeriya, Farfesa Babagana Umara Zulum ya dakatar da daukacin jami’an kiwon lafiyar da ke aiki a babban asibitin garin Ngala sakamakon yadda suka kaurace wa bakin aikinsu tare da barin majinyata cikin wani hali.

Talla

Wannan na zuwa ne bayan Zulum ya kai ziyarar ba-zata a asibitin a ranar Litinin da misalin karfe 11 na safe, inda ya tarar cewa, jami’an kiwon lafiyar sun mika ragamar kula da asibitin a hannu Kungiyar Agaji ta fhi360 da ke kula da daruruwan marasa lafiya ‘yan gudun hijira.

Jami’an lafiyar sun kaurace wa aikinsu duk da cewa suna karbar albashi daga hannun gwamnatin jihar Borno a kowanne karshen wata.

Gwamnan ya ce, nan kusa zai sake ziyartar asibitin, yana mai fatan ganin sauyin al'amura kafin dawowarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.