Najeriya-Jigawa

Almajirai za su fara karatun boko a Jigawa

Wasu daga cikin Almajirai a Najeriya
Wasu daga cikin Almajirai a Najeriya tribuneonlineng.com

Gwamnatin Jihar Jigawa da ke Najeriya ta ce, za ta sanya Almajirai dubu 1 da 322 a makarantun boko bayan wasu jihohin sun taso keyarsu zuwa gida sakamakon cutar coronavirus.

Talla

Gwamnan Jihar Muhammadu Badaru ya sanar da haka a yayin zantawa da manema labarai a Dutse game da halin da jihr ke ciki kan annobar.

A cewar gwamnan, ya bada umarnin yi wa Almajiran rajista a makarantun firamare don fara karatun boko, sannan kuma za su ci gaba da karatun Al-Kur’ani.

A can baya dai, gwamnan ya ce, Almajiran da aka maido da su gida daga wasu jihohin, na samun kyakkyawar kulawa, yayin da ya ce, 23 daga cikinsu da aka samu dauke da cutar coronavirus, yanzu haka suna ci gaba da karbar magani a cibiyar d a killace su.

Tuni aka mika sauran Almajiran ga iyayensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.