Najeriya

Ba mu da kudi da ma'aikata-Ministan Tsaron Najeriya

Sojojin Najeriya na fama da karancin ma'aikata da kudade duk da kalubalen tsaro a kasar.
Sojojin Najeriya na fama da karancin ma'aikata da kudade duk da kalubalen tsaro a kasar. premiumtimesng

Ministan Tsaron Najeriya, Bashir Magashi ya bayyna cewa, Rundunar Sojin kasar na fama da karancin ma’aikata da matsalar kudi duk da tarin kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.

Talla

A yayin zantawa da manema labarai a ranar Laraba jim kadan da kammala taron Majalisar Ministoci, Magashi ya ce, ya gabatar da wannan korafi a taron wanda aka gudanar ta kafar bidiyo karkashin jagorancin shugaba Muhammdu Buhari.

Magashi ya yi wannan korafin ne duk da cewa, a cikin shekaru biyar da suka gabata, Ma’aikatar Tsaron kasar na karbar kaso mai tsoka daga kasasfin kudin Najeriya, inda ake ba ta kudaden da suka zarce na bangaren ilimi da lafiya.

A kasafin bana kawai (wanda ake sa ran yi masa gyara), Ma’aikatar tsaron ta samu Naira biliyan 878 daga cikin Naira tiriliyan 10.59, ma’ana, ta samu kashi 8 cikin 100 na jumullar kudin kasafin.

Kodayake wasu jami’ai da dama da suka hada da Babban Hafsan Sojojin Kasar, Laftanar Tukur Buratai, sun sha korafin cewa, a mafi tarin lokuta, ba a ba su kudaden sayen makamai da na  gudanar da wasu ayyuka duk da cewa, an rattaba musu hannu a kasafin.

Sojojin Najeriya dai, na yaki da mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabshin kasar, da kuma ‘yan bindiga a yankin arewa maso yammacin kasar baya ga ‘yan tawaye da ‘yan fashin teku a kudu maso kudancin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.