Najeriya

Sama da mutane dubu 11 sun kamu da coronavirus a Najeriya

Sama da mutane dubu 11 sun kamu da coronavirus a Nejeriya.
Sama da mutane dubu 11 sun kamu da coronavirus a Nejeriya. Kola Sulaimon / AFP

Annobar coronavirus na ci gaba da yaduwa a Najeriya duk da kokarin hukumomin kasar na rage bazuwarta, yayin da jumullar mutanen da suka kamu da ita ta kai dubu 11 da 516.

Talla

A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, cutar ta harbi mutane 350 a sassan kasar kamar yadda Hukumar Yaki da Cutuka ta kasar, NCDC ta sanar a shafinta na Twitter.

Kimanin mutane dubu 3 da 535 sun yi katarin warkewa daga cutar, amma ta aika 323 lahira.

Wannan sabuwar annobar ta lakume rayukan mutane sama da dubu 387 a sassan duniya tun bayan bullarta a karshen shekarar bara a kasar China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI